<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>378</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Aure na masu bi aure ne mai tsarki, ku ƙaunace juna har abada
 Ubangiji Allah shi ne ya kafa aure ya ce mu yi aure a duniya

[V2]
 KORUS
 Ku zama ɗaya cikin zamanku, Amarya yi bayayya
 Ango ka ƙaunaceta gidan ku zai zama da Albarka

[V3]
 2) Ango na murmurshi, Amarya na murmurshi, dono yau suna cikin alkawali
 Mu masubi duka muna tayaku murna mune shaidun wannan aure a yau.
 Korus

[V4]
 3) Ku ba juna shawara juna yin addu'a, ku zuba ido ga Yesu Kristi,
 Ko cikin wahala ko cikin jin daɗi ku kasance da ƙaunan junan ku.
 Korus

[V5]
 4) Macen kirki takan faranta ran mijinta mara kirki takan zama ciwo
 Amarya ki zama mai faranta ran mijinki, mijinki zai kasance da murna.
 Korus

[V6]
 5) Samari da ƴan mata sai ku yi addu'a don ku yi nasara da magabci.
 Mu masu bi duka muna yin addu'a Ubangiji y baku nasara.
 Korus</lyrics>
<title>Aure Na Masu Bi, Aure Ne Mai Tsarki LW378</title>
</song>